<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ubangiji Allah, Ga Mu Nan Gabanka LW1</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ubangiji Allah, ga mu nan gabanka.
 Tun da farin hasken safe, mu ke nemanka.
 Muna yabon sunanka, ya Mai Iko Duka,
 Muna sujada, ya Mai Tsarki.

[V2]
 2) Ubangiji Uba, kai ne farkon kome,
 Kai ka ba da Ɗanka Yesu domin cetonmu.
 Mu da muka tayar, kai ka ji tausayinmu.
 Muna sujada, ya Mai Tsarki.

[V3]
 3) Ubangiji Yesu, kai ne Almasihu,
 Kai ka fanshi bayin Shaiɗan daga bautarsa.
 Kai ka ba da jininka domin mu mutane.
 Muna sujada, ya Mai Tsarki.

[V4]
 4) Ubangiji Ruhu, sunanka Mai Tsarki,
 Kai ne kana koya mana hanyar cetonmu.
 Kai ne jagabanmu, kullum sai mu bi ka.
 Muna sujada, ya Mai Tsarki.

[V5]
 5) Allah Ubangijinmu, ɗaya cikin uku,
 Harshe ba ya iya faɗin girman sunanka.
 Uba, Ɗa, da Ruhu, uku cikin ɗaya,
 Muna sujada, ya Mai Tsarki.</lyrics>
<hymn_number>1</hymn_number>
</song>